Game da mu

An samar da Africa academy ne da nufin taimaka wa al’umar Africa, wajen samun ingantacciyar fahimtar Musulunci, ta hanyar Alƙur’ani Mai girma, da Sunnar Annabi ﷺ.
Makaranta ce shakundum wadda ke gabatar da shirin ilimantarwa da nufin kusantar da ilimi zuwa ga masu sha’awar shi, ta hanyar Intanet, da kafofin sada zumunta, da kuma kan akwatin talabijin na Africa tv3.
Makarantar ta dogara da samar da ilimi mai zurfi a kan tsarin Massive Open Online Course wanda ake taƙaita shi da kalmar (MOOCs) Makarantar tana aiki ne 100%
ta Intanet inda ɗalibai za su iya shiga darussa ta hanyar kwamfuta da na’urori masu ƙwaƙwalwa, kuma suna iya halartar bitoci ta hanyar darussan da aka ɗauke su ta hanyar bidiyo da sauti da kuma littattafan PDF, da kuma amsa tambayoyin auna fahimta.
Kuma ta dogara da fitattunn malamai masu wa’azi na Ahlus Sunna wal Jama’a masu magana da harshen Hausa.

Buri

Muna burin mutum dubu talatin su shiga wannan tsarin a zango ukun farko.

Saƙo

Tsangatar Africa ta zamanto jagora a fagen koyarwa da harshen Hausa ta hanyar Internet, da hanyoyi na zamani, da kuma kafafen da suke da dangantaka da Tsangayar Africa, da sauran shafukan Intanet mabambanta.

Manufofi

1- Biyan buƙatar musulmai game da ilimin shari’a daga tushe, da kuma sanar da ɗalibi abin da dole ne a ce duk ɗalibin ilimi ya san shi, da harasan Africa.
2- Yaɗa aƙidar Ahlus Sunna wal Jama’a, da ingantaccen ilimin Fiƙihu tare da dalilansa na Ƙur’ani da Sunna.
3- Koyar da mata musulmai addininsu, da wayar da su, da kuma bayar da gudunmawa wajen horar da mata ɗaliban ilimin Shari’a.
4- Yaɗa wayewar koyon ilimin Shari’a ta hanyar Internet a Africa, ta hanyar samar da manhajar ilimi, wadda take kula da kwarewa, da ƙirƙira a wajen salon bijiro da ilimi.